Ma'aikatan gwamnati ne dai suka fi shiga cikin tasku, domin galibinsu, ba za su samu albashinsu ba, har sai bayan an kare hutu da za a yi cikin watan nan na Disamba.
Ma'aikatan lafiya da masu kayan sarki ne kadai, suka samu albashi kafin ranar Kirisimetin a ranar 21 ga watan nan, yayin da za a biya malamai a gobe, 28 ga wata, inda sauran kuma sai a ranar 3 ga watan Junairun sabuwar shekara.
Kamar kullum, 'yan fansho su ne a karshe, inda za a biya su a ranar 6 ga watan Junairun 2017, bayan an kammala bukukuwan.
Duk da ma'aikatan gwamnati ba sa farin ciki da wannan al'amari, gwamnatin ta tsinci kanta cikin matsalar rashin kudi, inda a kowanne wata take fafutukar biyan albashin dake lakume sama da kashi casa'in na kudin shigar kasar.
Ko a bara, hakan ce ta kasance, domin kuwa gwamnati ba ta biya ma'aikata ba sai bayan an kammala bukukuwan. (Fa'iza Mustapha)