Da yake jawabi ga taron shekara-shekara na magoya bayan jam'iyyar ta Zanu-PF a tsakiyar garin Masvingo, Mugabe, wanda shi ne sakataren jam'iyyar na farko, ya bayyana cewa jam'iyyar Zanu PF tana nan daram duk kuwa da irin makircin da ya ce 'yan adawar kasar, da kuma makiyan kasashen yammacin duniya suke nunawa gwamnatinsa.
Mugabe ya ce "jam'iyyarmu ta kasance mai karfi. Ba na tantama game da haka. Kasashen da suke nuna mana kiyayya, sun dauki tsawon lokaci suna kokarin ganin bayan wannan gwamnati, amma ba za su samu nasarar canza wannan shugabanci ba". (Ahmad Fagam)