An fara yin amfani da gadar Mohammed VI da kamfanin CREC na kasar Sin ya gina a kasar Morocco a jiya Alhamis. Sarkin kasar Morocco Mohammed VI ya yanke kyallen bude wannan gada.
Gadar ta ratsa kwarin kogi Bou Regreg, tsawonta ya kai mita 950, yayin da tsayinta ya kai mita 200.
Gadar Mohammed VI muhimmiyar gada ce dake kan hanyar kewayan Rabat, babban birnin kasar Morocco, tana da siffar musamman na gine-ginen Larabawa. Kafofin watsa labaru na kasar sun ba da labari cewa, wannan gada ta alamanta hadin gwiwar kasashen Sin da Morocco, za ta zama daya daga cikin muhimman gine-ginen kasar.
Darekta mai kula da aikin gina gadar Zhao Wenyi ya bayyana cewa, ba ma kawai kasar Sin ta gina wannan babbar gada ga kasar Morocco ba, hatta ma ta horar da kwararru da masu fasaha a fannin gina gada ga kasar, ta haka, kwarewar kasar Morocco wajen gina gada ta samu kyautatuwa sosai.(Lami)