Mabiya addinin Musulunci na gudanar da ibadar lahiya wato yanka dabbobi a duk shekara, wanda alama ce dake nuna kawo karshen aikin Hajji, bayan kammala tsaiwar Arafa a birnin Makka na kasara Saudiyya. A ranar Lititin musulmi kasar Morocco zasu bi sahun takwarorinsu na kasashen duniya domin gudanar da bukukuwan idin babbar sallah ta wannan shekara.
Game da batun barazanar tsaro a kasar ta Morocco, jaridar Al Ahdath Maghribiyya ta kasar ta rawaito cewa, akwai babbar barazanar kaddamar da hare haren ta'addanci daga kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci IS ke yiwa kasar.
Majiyar ta kara da cewar, akwai karin barazana game da tsaro da kasar ke fuskanta game da karuwar 'yan kasar Morocco dake nuna tausayi ga mabiya kungiyar masu kaifin kishin Islama a kasar, lamarin ya karawa kungiyar yawan magoya baya a kasar a 'yan watannin baya.
A cewar ma'aikatar cikin gida ta kasar Moroccon, sama da kungiyoyin 'yan ta'adda 160 ne aka tarwatsa a kasar daga shekarar 2002 zuwa yanzu, wadanda suke da alaka ta kut da kut da kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Syria da Iraqi ciki har da kungiyar IS.(Ahmad Fagam)