Matakan da aka tanada cikin takardun 2 sun hada da kara yawan masu gabatar da doka zuwa ofisoshin kwastan da hukumar kare kan iyaka, kara ikon ministan tsaron cikin gidan kasar kan matakan aiwatar da doka, gina ganuwa a bakin iyakokin Amurka da kasar Mexico da dai sauransu.
A ranar 27 ga watan jiya ne, shugaba Trump ya sa hannu kan wani umurni, inda aka hana 'yan gudun hijira na kasa da kasa da ma mutanen da suka fito daga kasashe 7 na yammacin Asiya da arewacin Afirka shiga Amurka. (Tasallah Yuan)