Wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari ya rabawa manema labarai ta bayyana cewa, shugabannin biyu sun kuma tattaunawa game da za su inganta matakan yaki da ayyukan ta'addanci ta hanyar samar da muhimman bayanai da sauran kayayyakin da ake bukata.
Mahukunta Najeriya sun bayyana cewa,tattaunawar ta yi armashi matuka, duba da yadda Trump din ya baiwa shugaba Buhari tabbacin Amurka na kulla sabuwar yarjejeniyar da za ta taimakawa Najeriya da makamai domin yakar ayyukan ta'addanci.
Bugu da kari, shugaba Trump ya jinjinawa shugaba Buhari game da kyawawan ayyukan da ya ke yi da kuma kokarinsa na kubutar da 'yan matan sakandaren garin Chibok 24 daga hannun mayakan Boko Haram da kuma namijin kokarin da sojojin Najeriyar suke yi a fannin yaki da 'yan tayar da kayar baya
Shugaba Buhari wanda ya ke hutu a birnin London tun ranar 19 ga watan Janairu inda ake duba lafiyarsu, ya yi amfani da wannan dama wajen taya shugaba Trump murnar nasarar da ya samu a zaben shugabancin kasar ta Amurka..
Shugaban Trump ne dai ya bukaci wannan tattaunawa da shugaban na Najeriya.(Ibrahim)