in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya nada sabon mataimaki kan harkokin tsaron kasa
2017-02-21 11:20:41 cri
A jiya Litinin ne shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da nada laftana janar Herbert McMaster, a matsayin mataimakin shugaba kan harkokin tsaron kasa, inda zai maye gurbin Michael Flynn wanda ya yi murabus a makon da ya gabata.

Mr.Trump ya sanar da hakan ne a gidan kansa dake jihar Florida, yana mai cewa Herbert McMaster, yana da basira da kuma fasaha ta gudanar da wannan aiki, kuma ana mutunta shi a rundunar sojan kasar.

A nasa bangare kuma, Mr. McMaster ya bayyana cewa, yana sa ran shiga tawagar kiyaye tsaron kasa, inda zai dukufa wajen kiyaye, da kuma kyautata yanayin tsaron Amurkawa.

A ranar 13 ga wata ne mataimakin shugaban na Amurka kan harkokin tsaron kasa Michael Flynn ya yi murabus, sabo da zargin da aka yi masa cewa furucinsa bai yi daidai ba yayin da yake tuntubar jakadan kasar Rasha dake kasar Amurka ta wayar tarho, lamarin da ya sa, ya kasance babban jami'i na farko da ya yi murabus bayan Donald Trump ya dare karagar mulkin kasa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China