Game da shirin da sojojin ruwa na kasar Amurka ke yi na tura jirgin yaki na ruwa samfurin USS Carl Vinson CVN-70 zuwa yankin tekun kudancin Sin don tabbatar da 'yancin zirga-zirgar jiragen ruwa, kana sun ce watakila za su shiga tekun dake dab da tsibirorin dake yankin, Geng Shuang ya bayyana cewa, tekun kudancin Sin da sauran tsibiran dake yankin mallakar kasar Sin ne. A saboda haka, ya kalubalanci kasar Amurka da ta guji daukar matakan da za su kawo illa ga 'yancin mallaka da tsaron kasar Sin, maimakon haka, kamata ya yi Amurkar ta girmama kokarin da kasashen dake yankin suke yi na tabbbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin baki daya. (Zainab)