A cikin wasikarsa ta yin murabus, mista Flynn ya ce, kafin ya kama aiki a hukumance, ya tuntubi wasu jami'an gwamnatocin ketare, da kuma jakadun kasashen waje da ke Amurka, ciki hadda jakadan kasar Rasha da ke Amurka. Mista Flynn ya amince da cewa, bai bayyanawa mataimakin shugaban kasar ta Amurka, cikakkiyar hirar da ya yi da jakadan Rasha ba, ko da yake bai yi hakan da gangan ko wata manufa ba. (Tasallah Yuan)