Sannan jaridar Vanguard ta Najeriya ta bayar da labara cewa, babban bankin Najeriya (CBN) ya fito da wasu sabbin matakan canjin kudaden ketare, a wani mataki na rage matsin lambar da kudin kasar wato Naira yake fuskanta kan yadda ake musayarsa a kasuwar bayan fage a halin yanzu.
Amma kuma duk da sabbin matakan da babban bankin Najeriyar ya bullo da su, yanzu haka ana sayan kowace dalar Amurka daya kan Naira 520 a kasuwar bayan fage.
Bugu da kari, jaridar "The Guardian" ta Najeriya ta labarta cewa, kungiyar kwadago a Najeriya ta yi Allah wadai da shirin da mahukuntan kasar Najeriya ke yi na sallamar ma'aikata 3,500 daga aiki, kan abin da gwamnatin ta ce an dauke su ne ba bisa ka'ida ba. (Ibrahim Yaya)