in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kai wa mutanen da ba su ji, ba su gani ba a Nijeriya
2017-02-18 12:33:37 cri
Ofishin MDD dake kula da batun agajin jin kai, ya bayyana damuwa kan harin da aka kai jiya, kan 'yan gudun hijira a wasu wurare biyu na birnin Maidugurin jihar Borno, dake arewa maso gabashin Nijeriya.

Mataimkin kakakin MDD Farhan Haq, ya ce har yanzu babu ainihin adadin wadanda suka mutu ko jikkata, sanadiyyar harin da Boko Haram ta kaddamar da bindigogi da ababen fashewa, a harabar ofishin kwastam da ke ba sama da 'yan gudun hijira dubu tara mafaka.

Haka zalika, ya ce an kai wani harin tashar mota ta Muna, inda 'yan gudun hijirar suka taru domin komawa gidajensu.

Ofishin ya tunatarwa da dukkan bangarori dake rikici a Nijeriya, su tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula kamar yadda dokokin kare hakkin dan Adam da na bada agajin jin kai na kasa da kasa suka tanada. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China