Cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, darakatan zartaswa na hukumar UNICEF Anthony Lake, ya ce lokaci na kurewa yara sama da miliyan guda, yana mai cewa, za a iya ceton rayukansu la'akari da cewa, ayyukan mutane ne suka haifar da matsalar ta yunwa da rashin abinci mai gina jiki.
Lake ya ce matsalar na bukatar daukin gaggawa, don gujewa maimatuwar matsalar da aka shiga a shekarar 2011 a kahon Afrika.
Adadin yara dake fama da rashin abinci mai gina jiki a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da ke yankin arewa maso gabashin Nijeriya mai fama da rikici, ka iya kai wa dubu dari hudu da hamsin a bana.
A karshen bara ne tsarin nan na Fews Net mai bibbiyar matsalar rashin abinci tare da yin gargadi da wuri, ya ce an yi fama da yunwa a wasu yankunan jihar Borno da ba a iya isa, kuma akwai yuwar matsalar ta ta'azzara har zuwa wasu karin yankunan da agajin jin kai ba sa iya isa. (Fa'iza Mustapha)