in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi ya gana da Rex Tillerson na kasar Amurka
2017-02-17 21:12:47 cri
A yau Jumma'a 17 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Mr. Wang Yi, wanda yake halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a birnin Bonn na kasar Jamus, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mr. Rex Tillerson.

A yayin ganawar tasu, Mr. Wang Yi ya bayyana cewa, zantawar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi da shugaban kasar Amurka Donald Trump ta wayar tarho, tana da muhimmanci matuka.

Ya ce bangaren Amurka ya yi alkawarin ci gaba da bin manufar kasancewar Sin daya tak a duniya. Kuma shugabannin kasashen biyu dukkansu suna ganin cewa, tabbas kasashen Sin da Amurka, za su ci gaba da zama abokan hadin kai na arziki. Don haka ne kuma, ya kamata a yi kokarin kara bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a sabon yanayin da ake ciki.

A nasa bangare kuma, Mr. Tillerson cewa ya yi, sada zumunci shi ne kadai matakin dake bayyana dangantakar dake tsakanin kasashen Amurka da Sin. Kaza lika bangaren Amurka na jaddada bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, ba ma kawai domin matukar muhimmancin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ba, har ma da fatan amfanin da za a samu, daga kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a yankin da suke ciki.

Ya ce bangaren Amurka yana fatan kara yin cudanya tsakanin manyan kusoshin kasashen biyu, domin kara bunkasa fahimtar juna. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China