Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, ya girke sabbin na'urori a filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa da ke garin Kaduna, ta yadda zai dace da zamani.
Shugaban kwamitin shirin mayar da harkokin jiragen sama daga filin saukar jiragen saman Abuja zuwa na Kadunan Muhammadu Joji shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai yayin rufe filin tashi da saukar jiragen sama na Abuja.
Sabbin na'urorin da aka saka sun hada da na'urar kula da tashin da saukar jiragen sama, da na'urar kula da kadawar iska da sauran na'urorin da su ke taimakawa a lokacin tashi da saukar jiragen sama. Kuma nan ba da dadewa ba za a fara gwada wadannan na'urori.
Bugu da kari, an dauki dukkan matakan tsaro da suka wajaba, don tabbatar da cewa, filin jirgin saman na Kaduna ya dace da duk na'o'in jiragen sama.
Joji ya ce, yanzu haka duk wani jirgin sama zai iya tashi da sauka a filin jirgin saman na Kaduna, yayin da aka rufe filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja har na tsawon makonni shida, domin gyara hanyar tashi da saukar jirage na filin.(Ibrahim)