Shugaba Xi ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Trump ta wayar tarho a yau Jumma'a, inda Xi ya bayyana manufar a matsayin muhimmmin batu ga dangantakar kasashen biyu.
Shugaba Xi ya ce Sin za ta yi aiki da Amurka, wajen bunkasa hadin kai da kuma tuntubar juna, domin dangantakar dake tsakaninsu ya kara habaka cikin kwanciyar hankali da lumana, ta yadda zai amfani al'ummominsu da kuma sauran al'ummar duniya.
A nasa bangare, Shugaba Trump ya ce ya fahimci muhimmancin da manufar kasar Sin kwaya daya ke da ita, yana mai cewa, Amurka za ta rungumi wannan manufa. (Fa'iza Mustapha)