in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara rage harajin masu sana'o'i domin rage musu nauyin gudanarwa
2017-02-09 10:17:57 cri

Majalissar zartaswar kasar Sin ta yanke shawarar sake rage wasu nau'o'in haraji da masu sana'o'i ke biya, a wani mataki na inganta hada hadar cinikayya, tare da ragewa masu sana'o'i nauyin gudanarwa.

Hakan dai na cikin matakan da ake aiwatarwa na raya sana'o'i a kasar Sin, yayin da kasar ke dada mai da hankali ga samar da daidaito a fannin ci gaban tattalin arziki, kamar dai yadda wata sanarwar bayan zaman majalissar na jiya Laraba ta ambata.

Rahotanni dai sun bayyana cewa, taron ya samu halartar kusoshin gwamnatin kasar Sin, ciki hadda firaminista Li Keqiang, wanda kuma shi ne ya jagoranci taron.

Tun cikin shekara ta 2013, manyan hukumomin kasar da kanana ke zaftare nau'o'in kudaden gudanarwa da suka kai 1,000. Sai dai majalissar zartaswar kasar ta lura cewa, har ya zuwa yanzu, akwai sauran wasu kudaden da ake cajin masu sana'o'i, wadanda ya zama wajibi a kankare su.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China