Wasu bayanai a hukumance, sun bayyana cewa a kasar Sin, an samu tashin farashin kayyaki a watan Janairu saboda hutun sabuwar shekara, yayin da farashin sarrafa kayyaki a kamfanoni ya karu, saboda tashin farashin mai da gas.
Hukumar kididdiga ta kasar ta bayyana cewa, alkaluman dake tantance farashin kayayyaki ya nuna cewa, farashin kayayyaki ya tashi da kashi 2.5 cikin watan da ya gabata, wanda ya dara kashi 2.4 da ake tsammani.
Tashin farashin ya haura kashi 2.1 da aka samu cikin watan Disamba, inda hutun sabuwar shekarar gargajiya ya yi sanadin karuwar farashin kayayyakin abinci da na sufuri.
A ko wane wata, a kan samu karuwar farashin da kashi daya cikin dari. ( Fa'iza Mustapha)