Cikin wata sanarwar da aka fitar bayan kammala babban taro kan kirkire-kirkire wanda ya gudana a jiya Talata ya nuna cewa, a halin yanzu, kamfanoni masu karfin fasaha a lardin na Guangdong sun kai 18,880 a shekarar 2016, inda aka samu karuwar kashi 78.8 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar 2015.
Hannayen jarin da gwamnatin Sin ta zuba a fannin kimiyya da fasaha a yankin ya kai kashi 88 cikin 100.
Bugu da kari, karuwar fasahar zamani da lardin na Guangdomng ya samu a shekarar da ta gabata ya kai kashi 50 cikin 100. (Ahmad Fagam)