in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kama daruruwan bakin haure a wasu sassan Amurka
2017-02-12 13:04:35 cri
Hukumomin kasar Amurka sun tabbatar da cewa, nan da mako daya da ya shige, hukumar shige da fice gami da kwastam ta kasar ta dauki matakai, na kama wasu daruruwan bakin hauren da suka shiga Amurka ba tare da samun izini ba.

Mai magana da yawun ma'aikatar tsaron cikin gida na Amurka Madam Gillian Christensen ta bayyana cewa, kamun da aka yi, wani mataki ne da aka dauka na yau da kullum, kuma akasarin bakin hauren da aka kama, sun taba aikata munanan laifuffuka, wadanda ke haifar da babbar barazana ga tsaron jama'a gami da tsarin shige da fice na Amurka. Amma Jaridar Washington Post ta ruwaito labarin dake cewa, akwai wasu bakin hauren da ba su taba aikata laifi ba, su ma aka kama su.

Ma'aikatar tsaron cikin gida, tare kuma da hukumar shige da fice gami da kwastam dake karkashin ma'aikatar, ba su bayyana adadin yawan bakin hauren da suka kama ba a cikin mako daya da ya shude. Amma kafofin watsa labaran kasar sun ce, daga ranar 6 zuwa 10 ga wata, an kama bakin haure su 161 a birnin Los Angeles, a birnin Atlanta ma, an kama bakin hauren kimanin dari 2. Bugu da kari, a biranen Chicago da New York ma an kama wasu bakin haure.

A ranar 25 ga watan Janairun bana, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya rattaba hannu kan wani umurni, na inganta harkokin tsaro a kan bakin iyakar kasa da daukar matakai kan makaurata, inda aka kara karfin yaki da bakin haure. Haka kuma idan an kama bakin haure da suka tsallake bakin iyaka, ba za'a sake su nan take ba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China