in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanin maganin gargajiya na Tongrentang na Beijing ya kafa reshensa a kasar Afirka ta Kudu
2016-11-25 10:47:04 cri
A kwanan baya, kamfanin maganin gargajiya na Tongrentong dake da hedkwatarsa a birnin Beijing na kasar Sin, ya kafa reshensa a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu a hukumance.

An ba da labarin cewa, nan gaba kamfanin Tongrentang na da shirin bude kantuna biyar a biranen Johannesburg, da Pretoria, da Durban na kasar Afirka ta Kudu, domin kara ba da hidimomi ga jama'ar kasar bisa samar da magungunan gargajiyar kasar Sin.

Dangane da lamarin, kansilan hukumar kimiyya da fasaha na ofishin jakadancin Sin a kasar Afirka ta Kudu, mista Huang Wei, ya bayyana cewa, yadda aka bude reshen kamfanin Tongrentang a kasar Afirka ta Kudu, wata muhimmiyar inshara ce da ta shaida shigowar magungunan gargajiyar kasar Sin cikin nahiyar Afirka. Bisa reshen kamfanin da aka kafa a kasar Afirka ta Kudu, kamfanin Tongrentang zai sa kaimi wajen harhada magungunan gargajiyar kasar Sin da ta Afirka, tare da fadakar da jama'ar nahiyar Afirka dangane da magungunan gargajiyar kasar Sin, domin kara kawo musu alheri.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China