in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An karrama jakadan Sin dake Afirka ta Kudu da lambar yabo a fannin aikin diflomasiyya
2017-02-13 10:57:00 cri
A kwanan baya ne, ma'aikatar harkokin wajen kasar Afirka ta Kudu ta shirya wata kasaitacciyar liyafar bayar da lambar yabo ta Ubuntu karo na uku a birnin Cape Town, inda ministar harkokin wajen kasar Madam Maite Nkoana-Mashabane, ta mika lambar yabo ta Ubuntu Oliver Tambo ga jakadan kasar Sin dake Afirka ta Kudun, Mista Tian Xuejun, saboda babbar gudummawar da ya bayar ta fuskar ayyukan diflomasiyya.

An lakabawa lambar yabo ta Ubuntu a fannin aikin jakadanci sunan Oliver Tambo, daya daga cikin fitattun shugabanni kana jami'an diflomasiyya a kasar Afirka ta Kudu.

A jawabinta, Madam Mashabane ta yaba matuka game da kokari da kuma babbar gudummawar da jakada Tian ya bayar ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka ta Kudun, inda ta ce, jakada Tian ya taka rawar gani a fannoni da dama, ciki har da habaka alaka gami da zurfafa hadin-gwiwa tsakanin Sin da Afirka ta Kudu, da taimakawa sosai wajen gudanar da taron koli na Johnnesburg na dandalin tattaunawar hadin-gwiwar Sin da Afirka, da tallafawa Afirka ta Kudu wajen samun bunkasar tattalin arziki da zamantakewar rayuwar al'umma.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China