in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya jajantawa takwaransa na Pakistan game da harin ta'addanci
2017-02-17 21:08:30 cri

A yau Jumma'a ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, ya aike da sako zuwa takwaransa na kasar Pakistan Mamnoon Hussain, yana mai jajantawa dangane da mummunan harin ta'addaci da aka kaddamar a yankin Sehwan na jihar Sindh.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce kasar Sin na adawa da ayyukan ta'addanci ta ko wane salo, tana kuma tir da wannan harin. Ya ce Sin za ta ci gaba da goyon bayan kokarin da Pakistan take yi, wajen yaki da 'yan ta'adda, da kiyaye kwanciyar hankali a kasar, da tabbatar da tsaron lafiyar jama'arta. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China