in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na shugaban Sin ya halarci bikin rantsar da shugaban Gambia
2017-02-19 13:26:16 cri

A Jiya Asabar ne manzon musammman na shugaba Xi Jinping na kasar Sin, kuma mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasar kasar mista Ma Peihua, ya halarci bikin kama aiki na shugaba Adama Barrow na kasar Gambia, wanda aka yi jiya a Banjul, babban birnin kasar.

Kafin bikin dai, Mista Ma ya gana da shugaba Barrow, inda ya mika sakon taya murna da fatan alkhairi na shugaba Xi Jinping.

Ma ya bayyana cewa, tun bayan farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen Sin da Gambia a watan Maris na bara, kasashen biyu sun farfado da dangantakar dake tsakaninsu a fannonin siyasa, tattalin arziki da cinikayya da al'adu da dai sauransu, inda ya ce sake kulla hudlar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu ya dace da zamani da moriyar jama'arsu.

Ya kuma bayyana kasarsa na karfafa hadin kai tare da sabuwar gwamnatin Gambia, don taimakawa kasar samun dauwamammen ci gaba.

A nasa bangaren, shugaba Barrow ya mika godiya ga shugaba Xi Jinping da ya aika da manzon musamman don halartar bikin kama aiki nasa.

Kana ya bayyana cewa, gwamnatinsa ta tsayawa kan manufar Sin daya tak, tare kuma da mai da Sin din aminiyrta ta kwarai. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China