in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar jami'an siyasa da na cigaba na MDD sun isa Gambiya
2017-02-16 10:48:46 cri
Wata tawagar jami'an MDD a fannonin siyasa da na raya cigaba sun ziyarci kasar Gambiya a jiya Laraba domin duba halin da ake ciki game da batun zaman lafiya da tsaro karkashin jagorancin sabon shugaban kasar.

Mai magana da yawun MDD Farhan Haq ya fada cewa, tawagar za ta duba yadda ma'aikatu da hukumonmin gwamnatin kasar suke gudanar da al'amurransu, domin nazartar irin tallafin da masu ruwa da tsaki na kasa da kasa za su baiwa kasar, kana da nazartar wuraren dake bukatar tallafin ayyukan MDDr domin cigaban hukumonin kasar da kungiyoyin fararen hula dake kasar.

Haq, ya kara da cewa, tun a ranar Talata ne tawagar ta isa kasar ta Gambia, sannan a ranar Laraba ta gana da shugaban kasar Barrow, bayan ta gana da mataimakinsa, da ministan harkokin wajen kasar, da jami'an MDD dake aiki a Gambia, da kuma jami'an diplomasiyya dake aiki a kasar ta yammacin Afrika.

A ranar 19 ga watan Janairu ne aka rantsar da Barrow a matsayin sabon shugaban kasar Gambian a ofishin jakadancin kasar ta Gambia dake Dakar, babbar birnin kasar Senegal. (Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China