in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ci gaba da kulla kawance da kasashen Afirka
2017-01-13 20:39:28 cri
Kasar Sin ta bayyana kudurinta na ci ga da kulla kawance da abokanta kasashen Afirka. Wadannan kalamai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya ke kammala ziyararsa ta farko a wannan shekara da ya kai kasashen Afirka.

Kakakin ma' aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya shaidawa taron manema labarai hakan a yau Jumma'a cewa, kasar Sin ta shafe shekaru 27, inda ministan harkokin wajenta ke fara kai ziyara kasashen Afirka a farkon ko wace shekara bisa al'ada.

A yayin ziyararsa wannan shekara, ministan harkokin wajen kasar ta Sin ya ziyarci kasashen Madagascar, Zambia, Tanzaniya, Jamhuriyar Congo da kuma tarayyar Najeriya.

Lu Kang ya bayyana cewa, wannan ziyara ta nuna cewa, karfada hadin gwiwa tsakanin kasashe maso tasowa ciki har da Afirka, tana kasancewa tushe na manufofin dflomasiyar kasar Sin.

Jami'in na kasar Sin ya kuma bayyana cewa, Sin da kasashen Afirka biyar din da ministan ya ziyarta, sun cimma yarjejeniya game da zurfafa hadin gwiwa, aiwatar da sakamakon taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka na Johannesburg da aka cimma a shekarar 2015 da kuma daga matsayin hadin gwiwar bangarorin biyu wato Sin da Afirka.

Haka kuma, shugabannin kasashen biyar sun jaddada kudurinsu game da martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya,kana sun yi maraba da gagarumar rawar da kazar Sin ta ke takawa a kokarin samar da zaman lafiya da ci gaba a nahiyar Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China