in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya bukaci a hada kai domin gina dadaddiyar dangantaka tsakanin Sin da Amurka
2017-01-18 11:18:41 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping a jiya Talata ya bukaci a tabbatar da hadin kai tsakanin Sin da Amurka domin ci gaba da dorewar dadaddiyar dangantaka dake tsakanin kasashen biyu, domin kasashen biyu su amfana da ma sauran kasashen duniya baki daya.

Shugaba Xi, ya yi wannan kiran ne a lokacin ganawa da mataimakin shugaban kasar Amurka Joe Biden a birnin Davos na kasar Switzerland.

Xi ya bukaci Biden ya isar da gaisuwarsa ta fatan alheri ga shugaban Amurkar Barack Obama.

An sha fuskantar sabanin ra'ayi game da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, sai dai kuma duk da hakan, al'amura na ci gaba da gudana a tsakanin kasashen biyu tun bayan da suka kulla yarjejeniyar huldar diplomsiyya shekaru 38 da suka gabata, in ji mista Xi Jinping.

Shugaban na Sin ya ce, dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin tana ci gaba da gudana yadda ya kamata, kuma kawo yanzu, an cimma nasarori masu yawa sakamakon hadin kan dake tsakanin bangaroron biyu, musamman tun lokacin da shugaba Xi da Obama suka cimma matsaya kan wasu yarjejeniyoyi bisa manyan tsare tsare tsakanin kasashen biyu sama da shekaru 3 da suka gabata.

Biden ya taya shugaba Xi murna, bisa muhimmin jawabin da ya gabatar a lokacin bude taron koli na kasashen duniya game da tattalin arziki na shekara shekara.

Kana ya gabatar da sakon Obama ga shugaba Xi Jinping, sannan ya yaba masa saboda kokarinsa na kara tabbatar da karfafa dangantakar dake tsakanin Amurka da Sin.

Game da alfanun dake tattare da dangantakar Amurka da Sin, Biden, ya bayyana cewa dangantakar kasashen biyu za ta haifar da moriya ga duniya baki daya a wannan karni na 21. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China