Mr. Wang ya bayyana hakan ne a jiya Talata yayin taron manema labarai, bayan kammala taron tattaunawa game da harkokin diflomasiyyar Sin da Australiya karo na 4.
Ya ce a matsayinta na mamban dindindin a kwamitin tsaron MDD, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan dukkanin tsare tsare na wanzar da tsaro da zaman lafiya a duniya. Kaza lika a matsayin kasa ta biyu a fannin karfin tattalin arziki, Sin za ta ba da cikakken taimako ga fadadar tattalin arziki duniya.
Minista Wang ya kara da cewa, ya zama wajibi kasashen duniya su yi hadin gwiwa, wajen magance kalubalen dake addabar duniya, ta hanyar biyayya ga dokokin da kasashen duniya suka tsare tsare cikin hadin gwiwa. (Saminu Hassan)