Mr. Yang wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya kara da cewa taron zai bada damar fidda managartan tsare-tsare, wadanda za su bada damar warware matsalolin da tattalin arzikin duniya ke fuskanta. Ya ce wasu daga cikin kudurorin da aka amince da su a yayin taron da su zamo irinsu na farko da taron ya cimma a tarihi.
Bugu da kari jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, taron ya baiwa mahalartan sa damar hada kai da juna, domin tinkarar matsalolin tattalin arziki da sauran kalubale na kasa da kasa. Haka kuma sakamakon gabatar da dabarun warware matsalolin da ake fuskanta a fannin kirkire kirkire da gyare-gyare, taron ya tanaji hanyoyin da za a bi don samar da tsarin ci gaba ta hanyar kirkire kirkire, da samar da ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030, karkashin tsarin kungiyar ta G20.
An dai fidda takardar bayan taro yayin rufe taron na G20 a jiya Litinin, takardar da ta fayyace hanyoyin wanzar da ci gaba filla filla, da dabarun cimma nasarar su bisa hadin gwiwar kasashe mambobin kungiyar. kaza lika an tattauna game da sauran batutuwa da ke shafar duniya baki daya, ciki hadda batun sauyin yanayi da kuma na 'yan gudun hijira. (Saminu)