Lu Kang ya bayyana cewa, manufar Sin daya tak a duniya ita ce babban ginshikin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka, wadda ta tabbatar da raya dangantakar yadda ya kamata. Sin tana fatan kasar Amurka za ta warware batun yankin Taiwan yadda ya kamata ta hanyar martaba manufar Sin daya tak a duniya da hadaddiyar sanarwa guda uku da Sin da Amurka suka bayar tare, wannan zai taimaka wajen tabbatar da ci gaba da yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata.
Game da batun ko za a kara yin mu'amala da hadin gwiwa a tsakanin Sin da Amurka bayan da shugabannin biyu suka tattauna da juna ta waya, Lu Kang ya bayyana cewa, a matsayinsu na manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya, kuma daya kasa ce mai tasowa mafi girma a duniya, yayin da dayan kuma kasa ce da fi ci gaba a duniya, akwai bukata da Sin da Amurka su fadada hadin gwiwarsu a fannoni da dama. (Zainab)