Mr. Sindimwo ya ce hakan ya zama dole, duba da yadda ake kin biyan dakarun na Burundi kudaden alawus din su, alhali kuwa ana biyan takwarorin su na kasashen Uganda da Kenya. Ya ce ko shakka ba bu, ba wata kasa ta kirki da za ta lamunci irin wannan nuna wariya.
Mr. Sindimwo na wannan jawabi ne yayin wani taron mane ma labarai, inda ya kara da cewa, muddin kungiyar hadin kan Afirka ta AU ba za ta rika biyan dakarun kasar sa hakkin su yadda ya kamata ba, to kuwa mahukuntan Burundi za su umarce su, da su fice daga tawagar ta AMISOM tare da dukkanin kayan aikin su.(Saminu Alhassan)