in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na matukar adawa da gwajin nukiliyar koriya ta arewa
2016-09-09 16:11:27 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta fidda wata sanarwa a Juma'ar nan, wadda ke nuna matukar adawar kasar ta Sin, da gwajin makaman nukiliya da kasar koriya ta arewa ke gudanarwa.

Sanarwar ta ce sam bai dace ba koriya ta arewan ta ci gaba da gwaje gwajen makaman nukiliya, duk da Allah wadai da hakan ke fuskanta daga sassa daban daban na duniya.

Kaza lika kasar Sin ta jaddada bukatar dake akwai ga koriya ta arewan, da ta martaba kudurin kwance damarar makaman nukiliya, kamar yadda hakan ke kunshe cikin kudurorin kwamitin tsaron MDD, domin kaucewa sake dagula al'amura a shiyyar.

Wani gidan talabijin mallakar kasar koriya ta arewan ya nuna yadda dakarun kasar suka gudanar da gwajin makaman nukiliya masu fashewa da sanyin safiyar yau din nan, gwajin da ya kasance irin sa na biyar da kasar ta gudanar, bayan watanni 8 da gudanar da makamancinsa.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China