Babagana Umara, shi ne kwamishina mai kula da sake giggina matsugunan da aka lalata a jahar, ya bayyana hakan ne a lokacin bikin kammala koyar da mata 18 sana'ar dinki a sansanin 'yan gudun hijira dake Wulari a birnin Maiduguri, na janar Borno.
Kwamishinan ya ce, za'a kafa cibiyoyin ne domin koyar da sana'oi ga mazauna sansanonin 'yan gudun hijirar, musamman mata wadanda za'a koyar da su sana'oi kala daban daban. Daga cikin sana'oin hannun da za'a koyar har da sana'ar kafinta, da walda, da seta wilin mota, da dinkin da dai sauransu.
Umara yace za'a dinga bada kudaden alawus na wata wata ga wadan da suka halarci kwas, da kuma abinci a kullum a tsawon lokacin gudanar da shirin, kuma shiri ne na hadin gwiwa da shirin raya cigaba na MDD wato (UNDP).
Rikicin Boko Haram yayi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 15,000 tun daga shekarar 2009, kana ya tilsatwa mutane sama da miliyan 2 kauracewa gidajensu.
Sai dai dakarun Najeriya, dake samun taimakon sojojin kasashe makwabta, sun yi nasarar kwace galibin yankunan da a baya mayakan na Boko Haram ke rike dasu.(Ahmad Fagam)