Manyan matakan da shugabannin G20 suka dauka a yayin taron kolin da aka kammala a ranar Litinin da ta gabata a Hangzhou, za su kawo tasiri mai armashi kan ci gaban nahiyar Afrika, in jin Alfred Dossou, wani masanin tattalin arziki dake aiki cikin wata jami'a mai zaman kanta dake Cotonou, babban birnin tattalin arzikin Benin.
A yayin wannan dandali, shugabannin G20 sun dauki matakan da suke shafar aiwatar da manufofi, tsare tsaren kirkirowa domin taimakawa bunkasuwa da zuba jari a fadin kasa da kasa, har ma da kokarin ganin bunkasuwar tattalin arziki ta amfanawa dukkan kasashe, da kuma kowa da kowa, in ji masanin.
A ganin wannan malamin jami'a a fannin nazarin tattalin arziki, wadannan matakai za su kawo tasiri kan ci gaban nahiyar Afrika dake bukatar abokan huldar tattalin arziki daga cikin wannan kungiya dake kunshe da kasashe 20 mafi karfin tattalin arziki a duniya.
A wannan lokaci, nahiyar Afrika dake kunshe da kusan biliyan daya na al'umma tare da wani adadin bunkasuwar da ta cimma kusan kashi 6 cikin 100 a tsawon shekaru biyar masu zuwa, na iya taka muhimmiyar rawa wajen warware kalubalolin duniya, har ma kuma da amsa muhimman bukatun kanta, musammun na wajen kyautata jin dadin al'ummominta, in ji mista Dossou tare da nuna cewa, domin fuskantar wadannan kalubaloli, nahiyar tana bukatar yin hadin gwiwa tare da kasashen G20.
Amma irin wannan dangantaka, kasashe nawa ne suke son samun ci gaba tare da nahiyar Afrika? Baya ga kasar Sin, kasa mai karfin tattalin arziki ce wadda ta bunkasa a wannan lokaci tare da kasashen Afrika bisa moriyar juna da adalci, in ji masanin tare da bayyana jin dadinsa kan zuwa Sin. (Maman Ada)