Rahoton bincikin ya nuna cewa, kashi 9 cikin 100 ne kawai na wadanda aka zanta da su suka nuna shakku game da makomar tattalin arzikin kasar ta Sin nan da shekaru biyu masu zuwa.
Alkaluma na nuna cewa, a rubu'in farko na shekarar 2016, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa da kaso 6.7 cukin 100, Kamar yadda masu sharhi suka yi hasashen cewa, a shekarar da ta gabata, tattalin arzikin kasar ta Sin zai bunkasa da kaso 6.7 cikin 100, karuwar da ta dara ta manyan kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
A hannu guda kuma, wani bincike da wani sashen nazarin tattalin arziki ya gudanar ya nuna cewa, ya zuwa karshen shekarar 2030, kudin shigar rukunin al'ummar Sinawa da ke matsakaicin matsayi zai karu daga kashi 10 cikin zuwa kashi 35 cikin 100.
Sai dai rahoton ya ce, duk da matsin lamba ta fannin aiki da jama'a ke fuskanta, hanyoyin biyan kudi na zamani irin sun a Alipay sun kara saukaka harkokin rayuwa. (Ibrahim)