in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bukaci a bullo da sabbin dabarun wanzar da zaman lafiya mai dorewa
2017-01-25 10:48:37 cri

A jiya Talata MDD ta bukaci a bullo da dabarun bai daya na samar da rigakafin tashe tashen hankula, da dakile duk wasu hanyoyin dake haifar da tashin hankali domin samar da dauwamamman zaman lafiya a duniya.

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya ba da jawabi mai takenmai taken gina dauwamamman zaman lafiya don amfanin kowa a yayin taron MDD, inda ya ce babbar hanyar da za ta tabbatar da samun dauwamamman zaman lafiya ita ce hada gwiwa don samar da dauwamamman cigaban al'umma.

Antonio Guterres ya ce akwai bukatar kasashen duniya su hada gwiwa wajen shawo kan makasudin dake haddasa tashe tashen hankula, kuma su bunkasa hanyoyin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da samar da dauwamamman cigaba da kare hakkin bil adama a matsayin wani muhimmin aiki na bai daya, kuma a aiwatar da wannan shirin a zahiri maimakon a takarda kadai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China