Yayin taron, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD mista Liu Jieyi ya ce, kafuwar asusun wani babban mataki ne da kasar Sin ta dauka da zummar zurfafa hadin gwiwa da MDD, kana wani mataki da kasar Sin ta dauka a ganin ta kara taimakawa majalisar baya, a kokarin da ta ke yi na tabbatar da zaman lafiya da cigaba a duniya.
Wakilin kasar ta Sin ya bayyana fatansa na ganin bangarorin Sin da MDD sun kara hada kai, don mai da asusun wani shahararren dandali ga hadin gwiwar bangarorin 2, tare da samar da gudummowa ga kokarin inganta ayyukan MDD, da raya harkokin da suka shafi bangarori daban daban na duniya, da wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya, gami da cimma burin daukacin dan Adam.
A nata bangare, Maria Viotti, darektan ofishin babban magatakardan MDD, ta ce majalisar tana godiya ga kasar Sin bisa tallafin da ta bayar cikin karamci. Ta kuma bayyana imani cewa, asusun zai taimakawa kokarin majalisar a fannonin kiyaye zaman lafiya da tsaro, da wanzar da samun ci gaba mai dorewa a duniya baki daya.(Bello Wang)