Da suke jawabi yayin wani babban taro kan inganta samar da magunguna a yankin kudu da hamadar Sahara, da kamfanin hada magunguna na Takeda ya shirya, ayarin kwararrun sun bayyana cewa, galibin marasa lafiya ba sa zuwa asibiti sai cuta ta ci karfinsu, suna masu alakanta matsalar da rashin wayewar kai game da batutuwan da suka shafi lafiya ko kuma rashin cibiyoyin kiwon lafiya.
A nasa bangare, shugaban Kamfanin hada magunguna na Goodlife, Josh Ruxin, ya ce an sanya biliyoyin daloli domin yaki da cututtuka irinsu kanjamau da zazzabin cizon sauro da tarin fuka a yankin, inda ya ce an kuma samu kyakyawan sakamako.
Sai dai ya ce al'amarin ya sauya a yanzu, inda cututtuka musamman wadanda basa yaduwa, kamar ciwon zuciya da sukari da cutar daji ke haddasa mace-mace.
Ya ce akwai bukatar inganta tsarin kiwon lafiya tare da kara warewa bangaren kudade da nufin kara inganta ayyukan kula da lafiya da kuma magunguna ta yadda za su isa ga jama'a. ( Faiza Mustapha)