Ministan ya bayyana haka ne jiya, a wajen babban taron kungiyar likitocin yara na shekara-shekara karo na 48 da ya gudana a jihar Kaduna dake yankin arewacin kasar.
Ya ce a yunkurinta na kara fadadawa tare da samar da ingantaccen kiwon lafiya, gwamnati ta fara aikin gyara cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda dubu goma dake fadin kasar.
Duk da cewa Nijeriya ta samu ingantuwar harkokin kiwon lafiya, ya ce akwai bukatar ta kara kaimi wajen kula da lafiyar yara musammam wadanda rikici ya daidaita.
A cewarsa, raguwar yawaitar mutuwar yara 'yan kasa da shekaru 5 daga dari da casa'in da daya zuwa tamanin da tara, da mutuwar jarirai daga casa'in da daya zuwa saba'in da biyar cikin kowacce haihuwa dubu daya, tsakanin shekarar 1990 da 2015, abun a yaba ne, duk da cewa har yanzu, ba a kai matakin da ake muradin kaiwa ba.
Isaac Adewole ya kuma kalubalanci mahalarta taron, sun lalubo shawarwari da za a yi amfani da su wajen kula da lafiya da sake tsugunar da yaran da rikicin ya daidaita da iyayensu.( Fa'iza Mustapha).