in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta bukaci kasashen Afirka su samar da karin kudade a fannin kiwon lafiya
2016-08-28 14:23:02 cri
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta bukaci kasashen Afrika dasu kara adadin kudaden da suke warewa a fannin kiwon lafiya.

Darakatan al'amurran kiwon lafiya da hulda da kasashen Afrika na hukumar WHO, Delanyo Dovlo, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewar, mafi yawan kasashen Afrika suna ware kaso 60 zuwa 70 ne na adadin kudaden da ake bukata a fannin kiwon lafiya na kasashen su.

Dovlo, ya fadi hakan ne a lokacin taron dandali na kungiyoyin lafiya na fararen hula na Afrika da aka gudanar a Nairobi.

Dovlo, ya kara da cewa, yawan amfani da tallafin kiwon lafiya da kasashen waje ke samarwa, duk da cewar ba laifi ba ne, amma yana jefa kasashen cikin rudani musamman game da makomar harkokin kiwon lafiyar kasashen nasu.

Ya bukaci nahiyar ta Afrika data kasance mai korari wajen kirkiro dabaru irin na zamani domin samar da isassun kudaden a fanin kiwon lafiya.

A shekarar 2001, kasashen Afrika sun fito da wata yarjejeniya ta Abuja Declaration, wadda aka amince kasashen Afrika su dinga ware a kalla kashi 15 cikin 100 na kasafin kudadensu a fannin kiwon lafiya.

Sai dai Dovlo yace, a halin yanzu, kasashe 6 kadai ne suka taba aiwatar da hakan sau daya ko abin da yayi kama da hakan, sannan kasashe 4 ne suke cigaba da aiwatar da yarjejeniyar.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China