Wannan sabon tsari na da burin yaki da Zoonoses wasu nau'in cututtukan da dabbobi suke yada wa mutane, da bazaranar kiwon lafiyar jama'a, da kyautata kiwon lafiya da jin dadin jama'a ta hanyar yin rigakafin haduruka da rage kaifin illolin da za su biyo baya.
Haka kuma wannan sabuwar manufa tana bada kwarin gwiwa wajen yin hadin gwiwa da amfana tare da dukkan bangarori da masu ruwa da tsaki wadanda ayyukansu na iya kawo wani tasiri kan kiwon lafiya, in ji ministar kiwon lafiyar Senegal, madam Awa Marie Col Seck a yayin bikin bude taron kwararru kan wannan manufa.
Bisa sakamakon ayyukan nasu, ministocin sun bukaci gwamnatocin kasashen Afrika dasu kafa wasu tsare tsaren gudanarwa masu karfi ta yadda za a tafiyar da wannan shirin yadda ya kamata.
Muna bukatar tsare tsare masu karfi da zasu taimakawa ga wata manufa ta bangarori daban daban, in ji madam Seck a yayin wani taron manema labarai.
Bayan wannan taron ministocin, muna jaddadawa domin ganin wadannan tsare tsare, sun rika la'akari da dukkan kiwon lafiyar jama'a, kiwon lafiyar dabbobi, har ma kuma da noma, kiwo da muhalli, in ji madam Seck. (Maman Ada)