in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya: ana bincike kan wasu makudan kudade da aka boye a gidan wani tsohon jami'in Gwamnati
2017-02-11 12:10:32 cri

Hukumar EFCC ta Nijeriya, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasar tu'annuti, ta ce ta fara binciken asalin wasu dala miliyan 9.8 da aka boye a gidan wani tsohon babban jami'in kamfanin mai na kasar wato NNPC.

Wata sanarwa da hukumar ta fitar a jiya Jumma'a ta ruwaito cewa, da yake amsa tambayoyin jami'an hukumar, tsohon Manajan Daraktan Kamfanin NNPC Andrew Yakubu ya tabbatar da cewa kudaden mallakinsa ne.

Sanarwar ta ce, an gano dalar na Amurka miliyan 9.8 da wasu fam dubu 74 ne a ranar 3 ga watan nan, yayin wani samame da jami'an hukumar suka kai gidan tsohon jami'in, a jihar Kaduna dake yankin arewa maso yammacin kasar.

Andrew Yakubu ya shaidawa masu binciken cewa, kudaden da aka samu a gidansa kyauta ce daga wasu mutane da bai bayyana sunayensu ba.

An dai boye makudan kudaden ne, cikin wani ma'ajiyi da aka boye a cikin gidan tsohon jami'in, dake unguwar Sabon Tasha a garin Kaduna.

Tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ne dai, ake wa tsohon jami'in da ya shugabanci kamfanin mai na kasar tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014 shari'a, bisa zarginsa da halasta kudin haram.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China