Ministan albarkatun man fetur na Nijeriya Ibe Kachikwu, ya ce ayyukan kungiyoyin tsageru masu lalata bututun mai a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur, na janyo wa kasar asarar dala biliyan tamanin a ko wace shekara.
Ya ce a ko wace shekara, ana samun matsalar ta lalata bututun mai sama da dubu goma a fadin yankin mai arzikin man fetur.
Ayyukan na tsagerun dai, ya janyowa kasar mummunar koma baya a tattalin arzikinta.
Ibe Kachikwu ya shaidawa manema labarai, jim kadan bayan kammala ganawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin yankin a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa mai arzikin mai cewa, gwamnati ta damu ainun, kuma tana kokarin shawo kan matsalar.
A cewarsa, an yi kiyasin cewa, yankin ya samu kudin shiga na kimanin dala biliyan talatin cikin shekaru goma, amma saboda ayyukan tsagerun, komai ya zurare, inda ake ci gaba da fama da talauci.
Har ila yau, Ministan ya bukaci mazauna yankin su rungumi batun hawa teburin sulhu da gwamnati. (Fa'iza Mustapha)