in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta fitar da shirin raya tattalinta nan da karshen watan Fabrairu
2017-02-04 09:40:30 cri
Gwamnatin Najeriya ta bayyana kudurinta na fito da shirin raya tattalin arzikin kasar(NERGP) nan da karshen watan Fabrairun wannan shekara idan Allah ya kai mu.

Mai magana da yawun ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na kasar Akpandem James wanda ya bayyana hakan a Abuja, fadar mulkin kasar, ya ce da zarar shirin ya kankama gwamnatin tana fatan samun bunkasuwar kaso 7 cikin 100 na tattalin arzikinta tsakanin shekarar 2017 zuwa 2020.

Shi dai wannan shiri na NERGP zai mayar da hankali ne kan manyan fannoni guda biyar, wato manufar tattalin arziki daga manyan fannoni, hanyoyin fadada tattalin arziki da kafofin da ke taimakawa ci gabansa, da batun yin takara. Sauran sun hada da hanyoyin inganta rayuwar jama'a da batun samar da guraben ayyukan yi da tsarin tafiyar da harkokin mulki da sauran fannonin da abin ya shafa.

Shugaban Najeriya Muhamnmadu Buhari ne ake saran zai kaddamar da shirin, Ana kuma saran gwamnati za ta tattauna da masana tattalin arziki daga sassa masu zaman kansu kafin a fara aiwatar da shirin.

Bugu da kari,ana saran za a tuntubi kwararru a fannin tattalin arziki, da sassa masu zaman kansu, da kungiyoyin fararen hula da malaman jami'o'i da kuma gwamnatocin jihohin kasar, a wani mataki na kara inganta wannan shiri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China