Wata sanarwa a hukumance mai taken "harkokin sararin samaniyar kasar Sin a shekarar 2016" ta ce kasar na mafani da sararin samaniyar ne ta hanyoyin da suka dace, tana mai cewa, tana daukar makaman kare sararin samaniyar domin tabbatar da dukkan harkokin da ake yi sun zama masu amfani ga bil'adama.
Sanawar, wadda ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar, ta ce gwamnatin kasar Sin ta dauki kamfanin da ke kula da sararin samaniyar a matsayi mai muhimanci wajen ciyar da kasar gaba.
A cewar sanarwar, nan da shekaru biyar, kasar Sin za ta ci gaba da aikinta na samar da sabbin manufofi da daidato, domin inganta kimiyya da fasahar ilimin sararin samaniya, ta yadda za su taimaka wajen kawo ci gaba tare da inganta rayuwar bil'adama. ( Fa'iza Mustapha )