in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za'a gudanar da zaben raba gardama a watan Afrilun bana a Turkiyya
2017-02-12 12:55:32 cri
Jiya Asabar, shugaban kwamitin koli mai kula da harkokin zabe na kasar Turkiyya Sadi Guven, ya sanar da cewa, za'a yi zaben raba gardama a ranar 16 ga watan Afrilun bana a kasar, inda za'a yanke shawarar ko za'a aiwatar da gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar ko a'a. Bisa wannan gyaran, za'a sauya tsarin siyasar Turkiyya daga tsarin majalisun dokoki zuwa tsarin shugaban kasa.

A shekaranjiya 10 ga wata, shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya amince da wannan shiri na gyaran fuskar ga kundin tsarin mulkin kasar, daga bisani kuma, ya yanke shawarar gudanar da zaben raba gardama kan wannan shiri.

Idan ana so a amince da wannan gyaran fuskar, ya zama tilas a samu goyon-bayan akalla kashi 51 bisa dari na daukacin al'ummar Turkiyya.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China