in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan sandan Turkiyya sun kama wadanda ake zargi da kasancewa 'yan kungiyar IS
2017-02-06 10:57:16 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Anadolu na kasar Turkiyya ta bayar, an ce a jiya Lahadi, 'yan sandan kasar sun kai wani samame kan wasu da ake zargin 'yan kungiyar IS ne mai tsattsauran ra'ayi, inda suka kama mutane 100 da ake zaton suna goyon bayan kungiyar.

An ce, 'yan sandan sun kama mutane 60 da ake zaton 'yan kungiyar IS ne a birnin Ankara, babban birnin kasar, wadanda akasarinsu 'yan kasashen waje ne. Har wa yau, an kama wasu 30 a lardin Konya da ke tsakiyar kasar, tare kuma da wasu 10 a lardunan Manisa, da Istanbul, da Samsun da Gaziantep.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China