in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha da Turkiyya za su inganta hadin gwiwa wajen yaki da IS
2017-02-10 10:54:14 cri
Kasashen Rasha da Turkiyya, sun amince da daukar karin matakai na inganta hadin gwiwarsu wajen yaki da kungiyar IS, da ma sauran kungiyoyin 'yan ta'adda a Syria.

Sassan biyu sun sha wannan alwashin ne, bayan da wani jirgin yakin kasar Rasha ya hallaka wasu sojojin Turkiyya su 3, tare da raunata wasu 11 bisa kuskure, yayin wani hari da ya kaddamar kan wani ginin dake garin Al-Bab inda aka jibje sojojin Turkiyya.

Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, shugaban Rasha Vladimir Putin, ya bayyana sakon ta'aziyya da jaje ga takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, game da aukuwar wannan tsautsayi.

Kaza lika shugabannin biyu sun amince da musayar bayanai na aikin soja, ta yadda za a kaucewa sake aukuwar makamancin lamari, yayin da suke ci gaba da fatattakar mayakan kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi a Syria. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China