Sai dai 'yan sandan ba su bayyana ainihin su wanene ba.
A wani labarin kuma, Jaridar Hürriyet ta Turkiyya ta ruwaito cewa, kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin a jiya Litinin.
Da sanyin safiyar ranar 1 ga wata ne, wani dan bingida ya kutsa kai cikin wani gidan rawa mai suna Reina, dake cibiyar birnin Istambul, inda ya yi harbin kan mai uwa da wabi, kan wadanda ke bikin sabuwar shekara.
Daga bisani dai dan bindigar ya tsere, amma a halin yanzu 'yan sanda sun dukufa domin farautarsa.
A wata sabuwa kuma, ma'aikatar harkokin cikin gidan Turkiyya ta sanar da cewa, a cikin makon daya da ya shude, 'yan sandan kasar sun tasa keyar mutane 47 da ake zargin suna da alaka da kungiyar IS, ciki har da wasu 25 wadanda aka riga aka cafke su.(Murtala Zhang)