Kamfanin dillancin labarai na Dogan ya rawaito cewa, jami'an 'yan sandan Turkiyya sun damke mutane 58 da ake zargin 'ya'yan kungiya mai fafutukar kafa daular musulunci ta IS ne, a lardunan Adana da Gaziantep dake kudancin kasar.
Rahotanni sun ce jami'an 'yan sandan sun yi amfani da jiragen saman helicopters na yaki da ta'addanci ne wajen kaddamar da bincike a wurare sama da 40 a lardin Adana, domin zakulo mayakan na IS.
Tuni dai aka garzaya da wadanda ake zargin zuwa hedkwatar 'yan sanda ta Adana don cigaba da bincike.
A wani labarin kuma, mayakan na IS 18 ne aka cafke a lokacin wani samame a lardin Gaziantep.
A shekarar 2016, kimanin mutane 3,359 ne aka kama a Turkiyya, yayin da mutane 1,313 daga cikinsu ake zargi da alaka da kungiyar IS. Kana cikin wadanda ake zargin mutane 679 'yan kasashen waje ne.(Ahmad Fagam)