in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
'Yan kasashen waje 28 aka kashe a harin da aka kai kasar Turkiya
2017-01-02 12:25:45 cri
Rahotanni daga kasar Turkiya na cewa, kimanin 'yan kasashen waje 28 daga kasashe daban-daban guda 9 ne aka kashe a harin da wani dan bindiga ya kai a wata mashaya a birnin Istambul na kasar ta Turkiya.

'Yan sa'o'i bayan harin ne shugaba Recep Tayyip Erdogan na kasar Turkiyya ya lashi takwabin ganin bayan ayyukan ta'addanci kwata-kwata a kasar.

Wani mamba a kwamitin sulhu na MDD ya yi allah-wadai da kakkausar murya a kan harin ta'addancin na ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2017 da aka kai a wata mashaya dake birnin Istambul na kasar Turkiya.

Rahotanni na cewa, yanzu haka 'yan sanda sun baza komarsu don zakulo dan ta'addanci da ya kai wannan hari, wanda ya zo haka ake nema ruwa a jallo.

Mahukuntan kasar Turkiyya dai sun bayyana cewa, mutane 39 ne suka mutu, kana wasu 69 kuma suka jikkata lokacin da wani dan bindiga ya bude wuta kan daruruwan mutanen da suka taru a mashayar ta Reina da ke gundumar Besikats yayin da suke shagulguan murnar sabuwar shekara. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China